A Libya, an karbe da iko da Bani Walid

Dakarun gwamnatin wucin gadin Libya, sun ce yanzu sun karbe iko da wajen garin Bani Walid, daya daga cikin garuruwa na karshe da ke goyon bayan kanar Gaddafi.

Sai dai kwamandojin 'yan tawayen sun ce sun fuskanci turjiya yayinda suka yi kokarin shiga garin ranar Lahadi.

Sun ce sun karbe iko da filin jirgin saman garin, da kuma sauran muhimman gine gine a garin.

A garin Sirte kuwa, har yanzu ana fafatawa ne da 'yan gani-kashenin Kanar Gaddafin da suka rage.