Biyan makudan kudaden ga 'yan majalisa ya sake tasowa

Majalisar dokokin Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

A Najeriya har yanzu makudan kudaden da akace 'yan majalisar dokokin kasar na karba a matsayin albashi da alawu alawus a kowanne wata na ci gaba da jan hankulan jama'a.

Ko a cikin rahotan da kwamitin da yayi nazari akan musabbabin tashe- tashen hankulan da suka biyo bayan zaben watan Afrilun shekarar ta 2011 wanda ke karkashin shugabancin Sheikh Ahmed Lemu ya fitar, ya gano cewar irin dumbim kudaden da 'yan majalisun kasar ke karba a duk wata na daga cikin irin abubuwan da suke tunzura jama'a.

Kwamitin Shekh Ahmed Lemun dai yace ya gano cewar makuden kudaden da 'yan majalisar kasar suke karba na ciwa akasarin 'yan kasar tuwo a kwarya.

To sai dai tuni wasu 'yan majalisun dokokin kasar suka soma maida martani game da wannan batu, inda suka musanta cewar suna karbar makudan kudade a matsayin albashi da alawu alawus a kowanne wata.