Clinton ta kai ziyarar ba-zata a birnin Tripoli

Clinton
Image caption Ita ce jami'ar Amurka mafi girma da ta je kasar

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta kai wata ziyara ta ba-zata a kasar Libya domin nuna goyon baya ga jama'ar kasar da kuma karfafa alakar kasashen biyu.

Ana sa ran Misis Clinton za ta shafe 'yan sa'o'i ne kawai a birnin na Tripoli.

Ita ce jami'ar Amurka mafi girma da ta kai ziyara kasar tun bayan boren da ya kai ga kifar da gwamnatin Kanar Gaddafi.

An boye ziyarar ta ta saboda matsalar tsaro, sannan kuma an tsaurara matakan tsaro a ko'ina domin shiryawa ziyarar.

Ziyarar ta na zuwa ne bayan wacce shugabannin Faransa da Burtaniya suka kai.

Misis Clinton za ta tattauna da manyan jami'an gwamnatin riko ta NTC - Shugaba Mustafa Abdul Jalil, Firayim Minista Mahmoud Jibril da Ministan Kudi Ali Tarhouni.

Za kuma ta yi wata ganawa da kungiyoyin mata da matasa da kuma na farar hula.

Jami'an Amurka sun ce ziyar ta nuna goyon baya ce ga jami'an NTC da kuma jama'ar kasar, da kuma kulla dangantaka mai karfi da kasar ta Libya.

Tun da farko a ranar Talata, an samu rahotannin gwabza kazamin fada a garin Sirte, inda magoya bayan Gaddafi ke ci gaba da nuna turjiya ga dakarun gwamnatin riko ta NTC.

Akalla dakarun NTC 1,000 ne suka kaddamar da hari a kan birnin ta gabas, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito.