Gilad Shalit ya isa Isara'ila

Gilad Shalit
Image caption Gilad Shalit lokacin da ake mikashi ga jami'an Isra'ila a Masar

Sojan Isra'ilan nan wanda ya shafe shekaru biyar a hannun Hamas, Gilad Shalit, ya isa gida bayan da Isra'ilar ta saki wasu daruruwan Palasdinawan da ta ke tsare da su.

An fara daukar Shalit ne daga Gaza zuwa Masar, inda aka mika shi ga jami'an Isra'ila, kafin daga bisani su tafi da shi gida.

Za a saki fiye da Palasdinawa 1,000 a karkashin tsarin musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da kuma kungiyar Hamas.

Za a saki kashin farko, 477, ranar Talata.

Dakarun Hamas sun kame Shalit ne a 2006, bayan da suka shiga Isra'ila ta karkashin kasa.

'Lafiya mai dorewa'

Tun da farko a ranar Talata ne aka dauki Gilad Shalit, dan shekaru 25, zuwa kan iyakar Gaza da Masar ta Rafa, inda aka mika shi ga jami'an Masar, amma a kan idon wakilan Isra'ila.

Daga bisani jami'an tsaron Isra'ila sun tabbatar da cewa ya na cikin koshin lafiya.

A hirarsa ta farko bayan sakinsa, Shalit ya shaida wa gidan talabijin na Masar cewa ya na cikin koshin lafiya, kuma ya yi farin ciki da ya samu kansa.

"Ina fatan dukkan sauran fursunonin da ake tsare da su za su samu 'yanci, abin da zai kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa ga bangarorin biyu," a cewar Shalit.

Su waye sukai nasara

Masu lura da al'amura na ganin musayar fursunar wata nasara ce ga kungiyar Hamas, ganin yadda ta tilastawa Isra'ila yin hulda da ita, bayan a baya ta ce ba za ta yi hakan ba.

A cewar Malam Uba Ahmed Jos, wani mai sharhi kan al'amuran Gabas ta Tsakiya, Hamas ta yi nasara kan Isra'ila da kuma kungiyar Fatah.

Amma ya ce akwai bukatar bangarorin biyu su hada kai domin cimma burinsu na samun cikakkiyar kasa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tun da farko wata majiya ta shaida wa BBC cewa dakarun Hamas na rike da Shalit, kuma za su mika shi ne kawai idan Palasdinawan sun riga sun bar Isra'ila.

Amma dai kuma an mika Shalit zuwa iyakar Kerem Shalom ta tsakanin Isara'ila da Masar.

Ya yi magana da iyayensa ta wayar salula inda ya shaida musu cewa ya na nan lafiya sumul kafin a dauke shi zuwa sansanin sojin sama na Tel Nof da ke Isra'ila.

A can ne kuma za a duba lafiyarsa sannan ya gana da danginsa da kuma Firayim Minista Netanyahu.

Fata nagari

Shi ma Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya ce ya na fatan wannan musayar fursunonin za ta taimaka wajen farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.

"Ina fatan wannan musayar za ta taimaka wajen farfado da shirin zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya," kamar yadda Ban ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a kasar Switzerland.

A gefe guda kuma, kashin farko na Palasdinawan su 477 sun shiga Masar daga Isra'ila ta Kerem Shalom, tafiyar kimanin mintuna 10 daga Rafah.

Sun bar wani gidan yari ne a Kudancin Isra'ila, yayin da ragowar suka fito daga wani gidan yarin a tsakiyar kasar - dukkansu dai karkashin tsauraran matakan tsaro.

An shirya za a saki ragowar fursunoni 550 a watan gobe.

Karin bayani