Rundunar JTF ta ba da wa'adin mika makamai

Wasu 'yan sanda a birnin Maiduguri
Image caption Wasu 'yan sanda a birnin Maiduguri

Rundunar tsaro ta JTF ta ba da wa'adin kasa da mako biyu, wadanda suka mallaki makamai ba bisa ka'ida ba su mika makaman.

JTF ta fidda sanarwan hakan ne a jihar Borno dake arewacin Najeriya, in da ta yi gargadin cewar duk wani wanda ya mallaki abubuwa masu fashewa ko makamai ba bisa ka'ida ba ya mika su ga shalkwatar JTF ko barikokin soji ko kuma shalkwatar hukumar leken asiri ta SSS da na 'yan sandan jihar.

Haka kuma rundunar ta bada nan da karshen watan Octobar da muke ciki da su mika wadannan abubuwan ko kuma su kuka da kansa.