Ana cigaba da taron likitoci kan cutar amodarin ido

Taswirar jamhuriyyar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar jamhuriyyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, yau ne aka shiga rana ta biyu na wani taron kwanaki uku da ya hada kwararrun likitoci masu aiki a fannin yaki da cutar amodari ko Trachoma wacce ke haddasa makanta.

Bayan nazari a kan ayyukan da suka aiwatar a tsawon shekarar da ta gabata, mahalartan za kuma su yi tsarin sabbin ayyukan da za su mayar da hankali a kai a wannan shekarar ta 2011.

Jihar Damagaram na daga cikin yankunan kasar da cutar ta amodari da ake dangantawa da rashin tsafta ta fi kamari, ko da yake an fara samun sauki akan lamarin.