Gilad Shalit ya sadu da 'yan uwasa

Gilad Shalit
Image caption Gilad Shalit

Sojan nan dan Isra'ila Gilad Shalit, wanda ya shafe fiye da shekaru 5 ana tsare da shi a Gaza, ya sake saduwa da iyalansa a wani sansanin mayakan sama dake Isra'ila.

Sajan Shalit, wanda ke da alamun gajiya, ya fadawa wani gidan talabijin na Masar cewa ya yi fama da kadaici, amma a kullum ya yi imanin cewa wata rana zaa sake shi.

A halin da ake ciki kuma, dubun dubatar Falasdinawa sun yi ta shagulgula a birnin Gaza domin murnar sakin kusan fursunoni dari 5 da Isra'ila ta yi a madadin sakin na Saja Shalit.

Sun samu kyakyawar maraba daga iyalansu da kuma shugabannin kungiyar Hamas.

Pira ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce an dauki lokaci mai tsawo ana tattaunawa kafin a cimma 'yarjejeniyar musayar fursunonin, wadda ya ce shawara ce mai wuyar sha'ani.