An kashe sojoji biyar a Syria

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

Masu fafutuka a Syria sun ce dakarun gwamnati sun kashe akalla mutane 21 a birnin Homs, birnin da aka sha yin zanga-zangar adawa da shugaba Bashar Al-Assad.

An kuma samu rahotannin kashe sojoji fiye da biyar a bata kashin da aka yi da wasu sojojin da suka bijire a garin Qusair dake kusa da kan iyakar kasar Lebanon.

Wasu sojojin da suka bijire sun shaidawa BBC cewa an basu umurnin kashe duk wani dan Syria da suka gani yana yawo akan titi.

Haka kuma wasu likitoci sun ce an yi barzanar kama su tare da azabtar da su muddin suka taimakawa mutanen da aka jiwa rauni sakamakon harbin bindiga.