Cutar zazzabin cizon sauro na raguwa a kasashe

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta fito da wani rahoto dangane da zazzabin cizon sauro ko Malaria.

Hukumar wadda ta gudanar da bincike a kasashe masu tasowa ta bayyana cewa yawan mutanan dake mutuwa ta wannan cuta sun ragu da kashe arba'in cikin dari.

A cewar hukumar hakan ya samu ne bisa wayar da kai da kuma samar da magungunan zazzabin na cizon sauro, a wasu kasashen.

Najeriya dai na daga cikin kasashen da jama'a ke fama da cutar zazzabin cizon sauron ko kuma Malaria, dan haka ko yaya lamarin yake a yanzu haka a kasar?