Ana yajin aikin gama-gari a Girka

Fira ministan Girka, Goerge Papandreou Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Fira ministan Girka, Goerge Papandreou

Ma'aikata a kasar Girka sun fara wani yajin aiki na kwanaki biyu don nuna adawa da shirin gwamnatin kasar na kara daukar matakan tsuke bakin aljihu da aka tsara da nufin shawo kan matsalar basussukan da suka yiwa kasar kanta.

A kwanaki biyun ana tunanin yajin aikin zai janyo tsayawar al'amura cik a kasar, inda za'a rufe shaguna kuma ma'aikatan filayen jirgin sama da sauran jama'a za su shiga cikin yajin aikin.

Ana sa ran 'yan Majalisun dokoki kasar za su kada kuri'a akan shirin rage albashin ma'aikata da rage kudaden fansho da kuma kara yawan haraji tare da rage yawan ma'akatan gwamnati a kasar.

Tuni dai 'yan kungiyar kwadago a kasar suka ce rage kudaden zai jefa kasar cikin wani mawuyacin hali.