Ana samun ci gaba a yaki da zazzabin cizon Sauro

Da alamun ana samun ci gaba a yaki da zazzabin cizon sabro ko malaria a duniya.

Daga farko dai an sami labarin cewa, mace-macen jama'ar da ake samu, sakamakon kamuwa da zazzabin, sun ragu.

Sannan kuma akwai yiwuwar cewa an gano rigakafin malariar, sakamakon wasu gwaje-gwajen maganin da aka yi.

A wannan makon hukumar Lafiya ta duniya ta ce an samu raguwar mutanen da ke mutuwa sakamakon cutar, da kashi ashirin cikin dari a shekaru goman da suka gabata.

Kasashe uku da suka hada da Morocco, da Turkmenistan da Armenia sun kawar da cutar baki daya.

Wani batu kuma shi ne na samun sabon maganin kawar da cutar, wadanda aka gwada a kasashe bakwai da ke nahiyar Afurka .