Matsalar fyade na karuwa a Najeriya

Tutar Najeriya
Image caption Tutar Najeriya

A Najeriya da alamu matsalar yiwa mata fyade na kara habaka sakamakon yadda al'amarin ke yawan aukuwa a sassa daban-daban na kasar.

Rahotanni sun ce wannan al'amari na aikata fyade kan rutsa har da mata tsofaffi tukuf, baya ga kananan yara.

Galibi dai ana ganin rashin fitowa a kai kuka ga hukumomi da kuma karancin hukunci mai tsanani a kan fyade ne ke taimakawa aukuwar matsalar.

Kungiyoyi masu zaman kansu dai na dora alhakin habakar matsalar akan rashin doka mai karfi na hukunta wadanda ke aikata laifin fyade a kasar.

Sai dai hukumomi a kasar na cewa suna iya bakin kokarinsu akan matsalar kuma akwai kudurin doka a gaban majalisar dokokin kasar da zai karfafa hukunci ga wadanda aka samu da laifin yin fyade.