ETA ta kawo karshen fafutuka a Spain

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar 'yan a-ware na neman 'yancin yankin Basque ne a Spaniya

Kungiyar 'yan a-ware ta Basque a Spain, ETA, ta ba da sanarwar abin da ta kira kawo karshen dukkan wata fafutuka da makamai.

A wata sanarwa, kungiyar ta ETA ta ce a yanzu an samu wata muhimmiyar dama don shimfida adalci da dimokuradiyya a Kasar Basque.

Gwamnatin Spain ta yi marhabin da wannan sanarwa.

Sai dai jangoran 'yan adawa masu ra'ayin mazan jiya, Mariano Rajoy, ya ce al'ummar Spain za su samu kwanciyar hankali ne kawai idan aka rusa kungiyar.

Wasu 'yan kasar ma sun nuna shakkunsu a kan sanarwar:

Wannan baiwar Allah ta cewa; "Zan so na ji sun ce ba za su kara ta da zaune tsaye ba har abada kuma ba za su sake kisa ba."