Tababa a kan yadda aka kashe Gaddafi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gawar kanal Gaddafi, bayan da aka kashe shi.

Ana ci gaba da shagulgula a Libya, bayan da aka kashe tsoshon shugaban kasar, Muammar Gaddafi, a kusa da mahaifarsa, wato Sirte.

Hotunan bidiyon da suka bayyana dai sun nuna Kanar Gaddafi a raye ko da yake ya yi jina-jina lokacin da aka kama shi.

Gwamnatin rikon kwaryar kasar ta musanta cewa kashe shi da gangan tana mai cewa harbinsa aka yi yayin wata musayar wuta tsakanin magoya bayansa da mayakan gwamnatin rikon kwarya.

An dai gano Kanar Gaddafi ne a boye a wata magudanar ruwa ga alama yana yunkurin tserewa daga Sirte a wani ayarin motoci wanda jiragen saman NATO suka kaiwa hari.

Kawo karshen harin NATO

Kwamandojin rundunar tsaro ta NATO za su gana yau Juma'a a brussels don tattuana yadda za a kawo karshen ruwan bama-baman da suka kwashe watanni bakwai suna yi a kan Libya.

Sakatare Janar na kungiyar ta NATO, Anders Fogh Rasmussen, ya ce bakin mulkin Kanar Gaddafi ya zo karshe bayan shekaru arba'in da biyar, al'amarin da ya kai ga babai na karshe a sa bakin da kungiyar ta yi a Libya.

Tun bayan fara kai hare-hare a watan Maris dai, kungiyar ta NATO ta yi barin bama-bamai har sau dubu ashirin da shida, kusan dubu goma daga ciki kuma da makamai masu linzami.

Martanin kasashen duniya

Kasar China ta bayyana mutuwar Kanar Gaddafi da cewa ta bude wani sabon babi a tarihin Libya.

Ma'aikatar harkokin wajen China ta yi kira a shimfida wani tsari na siyasa wanda zai kunshi dukkan al'ummar Libya da zarar damar yin hakan ta samu don tabbatar da hadin kan kasar.

Shugaban kasar Rasha, Dimitry Medvedev, ya ce yana fata Libya za ta rikide ta zama kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya cikin lumana.

Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon gargadi ya yi ga mutanen kasar ta Libya cewa za a fa sah wuya a kwanaki masu zuwa.

Shi kuwa Shugaba Hugo Chavez na Venezuela cewa ya yi Gaddafi ya yi shahada.

Ya ce; "Mun san Gaddafi jarumi ne iya tsawon rayuwarsa, kuma jagoran juyin juya-hali, yanzu kuma ya zama shahidi."