An kashe tsohon shugaban Libya Kanal Gaddafi - NTC

Kanal Gaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kanal Gaddafi ya shafe shekaru da dama yana mulkar kasar

Wani babban kwamandan dakarun gwamnatin riko ta Libya, ya ce an kashe tsohon shugaban Libya Kanal Mu'ammar Gaddafi a wani gumurzu a garin Sirte.

Ministan sadarwa Mahmoud Shammam ya ce mayakan sun shaida masa cewa sun ga gawar Kanal Gaddafi, yayin da wasu jami'an suma suka ce an kashe shi.

Rahotanni sun kuma ce an gano gawar dan Kanal Gaddafi Mu'atassim Gaddafi, wanda aka ce an kama shi ne tare da mahaifin na sa.

Har yanzu babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da rahotannin.

An kwashe makwanni ana dauki-ba-dadi a birnin na Sirte, wanda mahaifar shugaba Ghaddafi ne, inda yake da dimbin magoya baya.

Tun da farko wasu rahotanni sun ambato jami'an NTC suna cewa an kuma raunata Kanal Gaddafi a kafa.

Kanal Gaddafi ya karbi mulki ne a Libya a shekarar 1969.

An kuma kifar da gwamnatinsa ne bayan wani bore da aka fara a watan Fabreru.

Kotun hukunta laifukan yaki ta duniya ICC na farautarsa.

Bayani a gidan talabijin

Nato, wacce ta dade tana kai hare-hare ta sama kan Libya, ta ce ta kai hari ta sama a ranar Alhamis da safe kan wata masu goyon Gaddafi a kusa da garin Sirte.

Sai dai babu tabbas ko harin na Nato na da alaka da kisan na Gaddafi.

Ana sa ran shugaban gwamnatin riko ta NTC Mustafa Abdul Jalil zai yi jawabi ga jama'ar kasar ta gidan talabijin.

Mr Shammam ya ce shugaban NTC zai tabbatar da mutuwar Gaddafi a hukumance.

"An kashe shi a wani gumurzu da 'yan tawaye. Akwai hotunan da ke tabbatar da hakan," a cewarsa.

Wani hoton bidiyo na kaiwa-da-komowa a tsakanin dakarun NTC, wanda aka ce na gawar Kanal Gaddafi ne.

Wani jami'in na NTC, Abdel Hafez Ghoga, ya shaida wa AFP cewa: "Mun sanar da duniya cewa an kashe Gaddafi".

Karin bayani