Adawa da cire tallafin mai a Najeriya

Tankar mai ta NNPC Hakkin mallakar hoto google
Image caption Tankar mai ta NNPC

A Najeriya, har yanzu dai 'yan kasar na ci gaba da muhawara dangane da yunkurin gwamnatin kasar na janye tallafin da ake bayarwa ga farashin albarkatun man fetur daga badi.

Wasu dai na sukar wannan mataki, yayin da gwamnati ke cewa tallafin baya amfanar talakawa.

kuma janye shi zai samar da makudan kudaden da ake bukata domin samar da ababan more rayuwa ga jama'a.

Hon Bitrus Kaze dan majalisar wakilai ne dake sukar shirin janye tallafin kuma ya shaidawa BBC cewa yakamat talaka ya gani a kasa kafin gwamnati ta cire tallafin.