Wai shin wanene Kanal Gaddafi?

Gaddafi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kanal Gaddafi ya mulki Libya tun 1969

Mo`ammar Gaddafi ya hau karagar mulkin kasar Libya ne a watan Satumban shekarar 1969, lokacin da ya jagoranci wani juyin-mulkin da ba a zubar da jini ba, inda suka hambare gwamnatin Sarki Idris.

Yana da shekaru ashirin da bakwai da haihuwa ne lokacin da akidar mulki ta shugaban kasar Masar, Gamal Abdel Nasser ta shige shi.

Dabi`ar mafi yawan Shugabannin kasahen Larabawa ta rikidewa daga soja zuwa shugabannin kasa na farar-hula ta yi tasiri a kan shugaba Ghaddafi. Kuma ya fi sauran sa`o`insa dadewa a kan karaga.

Ya yi kokarin fitar da nasa salon mulki ko gwamnati a cikin kusan shekaru arba`in da daya da ya yi na mulkin kasar Libya ta hanyar tallafa wa `yan tawaye da masu ta da kayar-baya, irin su kungiyar IRA ta kasar Ireland ta arewa da Abu Sayyaf a kasar Philippines.

A wajajen karshen mulkinsa, an cire takunkumin da aka yi wa kasar Libya na mai da ita saniyar-ware sakamakon wani harin bom din da ya tarwatsa jirgin saman Pan Am a Lokerbie na kasar Scotland, a watan Disamban shekarar 1988.

Jamahiriya

Kuma janye takunkumin ya yi sanadin kwararar kasashen yamma da kamfanoni zuwa kasar domin ayyukan kwangila a fannin mai da makamashi.

An fara rikicin da ya yi sanadin kifar da gwamnatinsa ne a watan Fabrairun shekara ta 2011 a birnin Benghazi, wanda shi ne na biyu a tsakanin manyan biranen kasar Libya.

Kazalika shi ne birnin da ake zargin cewa shugaba Ghaddafin bai ba shi wata kulawa ta sosai ba.

Harwayau, ana zargin cewa shugaba Ghaddafin bai yarda da mazauna birnin ba a iya zamanin da ya yi yana mulki.

An haifi shugaba Ghaddafi ne a garin Sirte, a shekarar 1946 ga zuriyar Badawi. Ya kasance mai alfahari da asalin kabilarsa. Yakan so ganawa da bakinsa a cikin tantinsa, wanda yakan kafa ko da ya kai ziyara kasashen waje.

Da farko ya kafa gwamnatinsa ne a kan akidar kyamar Turawan mulkin mallaka, wanda daga bisani kuma ya ci gaba da tafiyar da kasar a kan tafarkin juyin-juya-hali.

Akida ko falsafarsa ta siyasa na cikin wani kundi mai suna "Green Book" wanda ke bayyana gwamnatinsa da "gwamnatin talakawa."

A shekarar 1977 shugaba Ghaddafi ya ayyana kasar Libya a matsayin Jamhiriya, wato kasar talakawa. Wato gwamnatin kasar Libya ta zama ta dimokuradiyya, wadda majalisar juyin-juya-hali ke mulkinta.

Amma a zahiri, shugaba Ghaddafi ne ke yanke duk wata muhimmiyar shawara a kasar. Haka kuma baki dayan dukiyar kasar na hannunsa, shi ne ke da wuka-da-nama.

Mu`amala ko huldodinsa

Ghaddafi kwararren dan siyasa ne mai matukar dabara, wanda kan gwara kan kabilu bangarorin kasar da juna. Haka kuma kafa kansa sosai, har ta kai ga ya zama kamar wani karfen-kafa. Kazalika shi ke iko da `yan sandan kasar a zamanin mulkinsa.

Wani lokaci da za ce shi ne mafi tsauri ga al`umar kasar shi ne lokacin da ya gwada wani tsarinsa na walwalar jama`a a kan al`umar kasar, a shekarar 1980 da `yan kai.

Ya kuma haramta dukkan kamfanoni na `yan kasuwa ko masu zaman-kansu da duk wadansu litattafan da ba a gamsu da abubuwan da suka kunsa ba a kasar a sauye-sauyen da ke kunshe cikin manufofinsa na juyin-juya-hali ta fuskar al`adu.

Ya kuma tabbatar da cewa ya halaka dukkan masu adawa da shi na kasashen waje. An kuma haramta `yancin fadar albarkacin baki da na hulda ko mu`amala da jama`a ko kafa kungiyoyi da kuma tauye hakkin jama`a da musguna musu.

Ana cikin wannan halin ne kuma sai kasashen yamma suka saka wa kasar Libyan takunkumi, inda aka mai da ita saniyar-ware sakamakon harin bom na Lokerbie.

Ga masu sukar Kanar Ghaddafi dai, babban laifinsa shi ne yadda ya yi ta facaka da dukiyar kasar wajen tafiye-tafiye da mu`amala da wasu kasashen waje da kuma matsalar cin hanci da rashawa.

Kasar Libya dai na da yawan al`umar da bai wuce miliyan shida ba. Kuma ta samu kudin-shiga daga mai da ya kai dala miliyan dubu talatin da biyu a shekara ta 2010. Wannan ya sa ana ganin cewa kasar tana da arziki mai yawa.

Mafi yawan `yan kasar dai ba sa cin gajiyar wannan arzikin. Kuma rayuwarsu ba ta da bambanci da ta al`umomin kasashen da ke fama da talauci.

Image caption Saifi Islam na daga cikin manyan 'ya'yan Kanal Gaddafi

Matsalar rashin aikin yin da ake fama da ita baya ga aikin gwamnati ta kai kashi talatin bisa dari ko ma fiye.

Akidar mulkin gurguzun da kasar Libya ke bi ba ta bai wa `yan kasar damar samun ilimi da kiwon lafiya kyauta , ko kuma muhalli da sufuri a farashi mai rangwame ba.

Dadin dadawa, ana fama da karancin albashi, kuma wasu kalilan ne ke cin gajiyar arzikin kasar da kuma ribar da take samu daga jarin da kasashen waje ke zubawa.

A shekarar 1999 ne aka kawo karshen matakin da kasashen yamma suka dauka na maida kasar Libyan saniyar-ware bayan shugaba Ghaddafi ya amince da zargin da ake masa na kai harin bom na Lockerbie.

Bayan harin sha daya ga watan Satumba, shugaba Ghaddafi ya cimma yarjejeniya da Amurka lokacin da ta yi yaki da ta`addanci. Kuma lokacin da Amurka ta mamayi kasar Iraki a shekara ta 2003 sai kasar Libya ta sanar da cewa ta yi watsi da shirinta na makamin nukiliya.

A karshen shekarun mulkinsa, maganar kokawar wanda zai kasance magajin shugaba Ghaddafin ta kaure tsakanin `ya`yansa biyu. Da Saif-al Islam da Mu'tassim.

Tasirin babban dan nasa, Saif-al Islam, wanda ya fi mai da hanakali wajen kafafen yada labarai da kare hakkin bil`adama ya ragu, yayin da na Mu'tassim, wanda ke da karfi a bangaren tsaro ya karu.

Al`umar kasar Libya dai sun yunkura sun kifar da gwamnatin shugaba Ghaddafi sakamakon tasirin da makwabtan kasar gabashi da yammaci suka yi a kansu, suka kawo karshen mulkinsa na kama-karya.