Kungiyar NATO za ta karashe aikinta a Libya

Shugaban dakarun kungiyar tsaro ta NATO ya ce yana goyan bayan da a kawo karshen aikin kawancen a Libya bayan mutuwar kanar Gaddafi.

Admiral James Stavridis ya bayyana hakan ne gabanin wani taron manyan jami'an kungiyar NATO din da za a yi a Brussels.

A wajen wannan taro ne za su tattauna kan hare hare ta sama da ta ruwa da suka kwashe watannin bakwai suna kaiwa akasar ta Libya.

Wakilin BBC ya ce jakadun kungiyar tsaron ta NATO sun amince za a iya kawo karshen ayyukan nasu a kasar, amma kuma ba nan take hakan zai faru ba.