Omran ya dauki alhakin mutuwar Gaddafi

Tutar 'yan tawayen Libya
Image caption Tutar 'yan tawayen Libya

Kwamandan mayakan Majalisar wucin gadin Libya da suka kama Kanar Muammar Gaddafi, ya ce ya dauki alhakin mutuwarsa.

A wata hira ta musamman da BBC ta yi da shi, Omran el Oweib ya ce an zakulo ne Kanar Gaddafi ne daga wata magudanar ruwa inda ya buya, kuma bayan ya yi tafiya ta taku goma, ya yanke jiki ya fadi, bayan da wani gungun mayaka da suka fuskata, suka afka ma shi.

Mr el Oweib ya ce ba za a iya tantance wanda ya harba harsashin da ya zama ajalinsa ba.

Ya ce ya yi kokarin ceton ran tsohon shugaban na Libya, amma ya cika a cikin wata motar daukar marasa lafiya, yayinda ake kokarin kai shi wani asibiti dake wajen birnin Sirte.