Za a yi zabe a Libya nan da watanni takwas

Praministan rikon kwaryar Libya, Mahmoud Jibril ya ce za a gudanar da zaben farko a kasar nan da watanni takwas masu zuwa.

Yayinda yake magana a lokacin wata ziyara da ya kai Jordan, Mr Jibril ya ce jama'ar Libyar za su fara zabar 'yan majalisar dokoki ne, wadda ake kira National Congress:

Ya ce, majalisa tana da ayyuka biyu ne. Na farko, shata daftarin tsarin mulkin kasar, wanda kuma jama'ar kasar za su kada kuri'ar rabagardama a kai.

Aiki na biyu kuma shi ne kafa wata gwamnatin rikon kwaryar da za ta mulki kasar har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasa.