Har yanzu ba a binne gawar Gaddafi ba

Masu layin kallon gawar Gaddafi a Misrata Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu layin kallon gawar Gaddafi a Misrata

Kwanaki biyu bayan kashe tsohon shugaban Libya Kanar Gaddafi har yanzu ana ci gaba da tababa kan yadda za a yi da gawarsa.

Akwai dai alamun sabanin ra'ayi tsakanin kungiyoyi daban daban da suka hambaras da gwamnatin Gadafin, kan yadda za a yi da gawar tasa.

An ajiye gawar ne a wani gidan kankara na ajiye nama a birnin Misrata, kuma har ta fara alamun rubewa.

Ana sa ran wani mai bincike kan musabbabin mutuwa, zai binciki gawar Kanar Gaddafin, don gano abin da ya zamo ajalinsa.

Sai dai wasu kwamandojin soja a Misrata sun ce ba za a taba bincika gawar ba.