'Yan Nijar sun zargi gwamnati da kasa mangance yunwa

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Jamhuriyar Nijar

Wasu jama'a a jamhuriyar Nijar sun zargi gwamnatin kasar da kasa yin katabus don magance matsalar yunwar da ta ke tunkurar kasar.

Rahotanni sun ce mai yiwuwa kasar ta fada cikin matsalar karancin abinci sakamakon matsalolin da suka biyo bayan daminar bana.

Kawo yanzu dai, baya ga kwamitin da gwamnatin kasar ta ce ta kafa don tunkurar matsalar, babu wani yunkuri na zahiri da ake ganin ta fara don magance matsalar.

Sai dai gwamnati ta ce tana son samun tallafin kudi ne don shawo kan matsalar.

'Yan kasar dai sun yi kira ga gwamnatin ta kwace kudaden da ake zargin wasu 'yan kasar da sacewa, kana ta yi amfani da su wajen magance wannan matsala.