Jama'a sun fito sosai a zaben Tunisia

Rahotanni daga Tunisia sun ce mutane da yawa sun fito don kada kuri'a a zaben da aka yi a kasar, wanda shi ne na farko da ake yi bisa gaskiya da adalci a Gabas Ta Tsakiya, tun bayan da Guguwar

sauyi ta fara kadawa a kasashen Larabawa, kasa da shekara daya da ta wuce.

An bar wasu rumfuna zabe a bude, bayan lokacin rufe su ya yi, domin ba jama'ar dake ciki layi damar jefa kuriarsu.

An kiyasta cewa kashi 70 daga cikin 100 na masu zabe ne fito don kada kuria.

Ana zaben 'yan majalisar dokoki ne, wadanda za su shata daftarin wani sabon tsarin mulkin kasar da kuma nada shugaban kasa, wanda shi kuma zai kafa wata sabuwar gwamnati.

Juyin juya hali a Tunisia dai ya fara ne watanni 10 da suka wuce, bayan wani matashi Mohammed Bouazizi, ya cinna wa kansa wuta, don nuna takaicin sa da gwamnati.

Hakan ya haifar da wasu boren a wasu kasashen Larabawa, wadanda suka kai ga hambarar da shugabannin Masar da kuma Libya.