An sake kai hari a jihar Kaduna

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

A jahar kadunan Najeriya, wasu mutane da baa san ko su wane ne ba sun kai hari a garin katari dake karamar hukumar kagarko.

Maharan sun je garin ne a wata karamar mota, inda suka yi harbe a kasuwar garin,suka kuma kashe mutane biyu, ciki har da wani dan sanda.

Wannan ne dai karo na biyu a baya-baya nan da wasu wadanda baa tantance ba suka kaddamar da hare- hare a jahar.

A karshen mako ma wasu 'yan bindiga sun kai hari a garin Saminaka na karamar Hukumar Lere inda suka halaka mutane biyu, kuma suka kona offishin 'yan sanda da wawashe wani banki.

Matsalar rashin tsaro dai ta zaman ruwan dare a Najeriya, duk kuwa da matakan da gwamnatoci ke cewa suna dauka.