Ana ci gaba da kirga kuri'u a Tunisia

Ana ci gaba da kirga kuri'u a Tunisia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mahukunta sun ce jama'a sun fito sosai don kada kuri'a

Jami'an zabe a kasar Tunisia na ci gaba da kirga kuri'un da aka kada a zaben da aka gudanar ranar Lahadi, wanda shi ne na farko tun bayan boren kasashen Larabawa. Fiye kashi 90 cikin dari ne na wadanda suka yi rijista suka fito domin kada kuri'a, a cewar mahukunta.

'Yan kasar ta Tunisia na zaben 'yan majalisu 217- wadanda za su rubuta sabon tsarin mulki sannan su zabi shugaban riko, wanda zai kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya.

Jam'iyyar masu matsakaicin ra'ayin Islama Ennahda ce ake sa ran za ta lashe yawancin kujerun, amma ba za ta samu rinjayen da take bukata ba.

"Bamu haura kashi 40 a cikin dari ba - mai yiwuwa mu haura ko kuma mu gaza hakan da kadan," kamar yadda Samir Dilou, wani babban mamba a Ennahda ya ce, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.

'Muhimmin mataki'

Amurka da Tarayyar Turai sun jinjinawa Tunisia kan yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, inda Barack Obama ya bayyana shi da cewa "wani muhimmin mataki ne".

Watanni tara da suka wuce ne aka hambarar da gwamnatin shugaba Zine al-Abidine Ben Ali sakamakon zanga-zangar neman sauyi - bayan ya shafe shekaru 23 yana kan karagar mulki.

Sakatare janar na Hukumar Zaben kasar Boubaker Bethabet ya ce fiye da kashi 90 na mutane miliyan 4.1 da suka yi rijista ne suka kada kuri'a. Babu wani kiyasi na mutane miliyan 3.1 da basu yi rijista ba wadanda kuma na da 'yancin kada kuri'a.