Amurka ta janye jakadanta a Syria

Robert Ford Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A kwanakin baya an jefi Robert Ford da tumatir da kwai

Amurka ta janye jakadanta a Syria Ambasada Robert Ford, saboda barazar tsaro da yake fuskanta. Dama ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin kasar.

Can dama dai Ambasada Robert Ford, yayi kaurin suna wajen sukar irin matakan da gwamnatin Syria ke dauka akan masu zanga-zanga da suka yi watanni bakwai suna nuna adawarsu da mulkin Shugaba Bashar Al-Asad.

Wani kakkakin ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ya ce bawai anjanye jakadan kenan daga Syria ba, amma kuma maido dashi zai danganta ne akan yanayin tsaron kasar.

Har yanzu dai ba a fayyace dalilin da ya sa kasar Amurka ta janye Robbert Ford daga kasar Syria ba.

Sai dai a `yan makwannin nan ya kasance wanda akan kai wa hari a duk lokacin da ya fita waje.

Magoya bayan gwamnatin kasar Syria da kan yi zanga-zanga sun sha jifansa da kwayaye ko tumatir don nuna takaicinsu game da alakarsa da jigogin masu adawa da gwamnati da kuma yadda Amurka ke fitowa baro-baro tana sukar gwamnatin shugaba Al`asad.

Watakila ganin yadda zaman zullumi ke karuwa a kasar ne ya sa gwamnatin Amurka ta yanke shawarar cewa zai yi kyau jakadan nata ya bar kasar.

Kasashen Burtaniya da Faransa dai ba su fito sun yi wa shugaba Al`asad din zazzafar suka ba, amma ana sa-ido a kan jakadunsu.

Kuma ofishin harkokin wajen Burtaniya ya ce babu wani shirin janye jakandan Burtaniyar daga kasar ta Syria.