'Syria na gallazawa 'yan adawa'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

Kungiyar kare hakkin bil adama ta duniya, Amnesty International, ta ce gwamnatin Syria ta mayar da asibitocin kasar wajen da take gallazawa 'yan adawa a yunkurin da take yi na dakatar da zanga-zangar kin jininta da ake yi.

A wani rahoto da ta fitar yau Talata, kungiyar Amnesty international, ta ce akasarin mutanen da suka samu raunuka a lokacin zanga-zanga na tsoron zuwa asibitocin kasar, saboda rahotannin da ke cewa jami'an tsaro na yin awon-gaba da mutanen da suka je karbar magani, sannan su azabtar da su.

Likitoci sun shaidawa kungiyar cewa yanzu haka masu zanga-zangar sun gwammace zuwa asibitoci masu zaman kansu, wadanda kuma basu da isasshen jinin da za su rika karawa masu fama da munanan raunuka.

Sun ce hakan ya sanya mutanen da basu samu kulawa ba suna mutuwa.