An gano wata jaririya a karkashin gini a Turkiyya

An gano wata jaririya a karkashin gini a Turkiyya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har yanzu ana ci gaba da ayyukan ceto

An gano wata jaririya 'yar mako biyu da haihuwa a raye bayan ta shafe kwanaki biyu a karkashin kuraguzan gine-gine biyo bayan girgizar kasar da aka yi a kasar Turkiyya.

Mahaifiyar yarinyar wacce itama ke makale a karkashin gini, a yanzu an ceto ta.

Gidaje kusan 2000 ne suka rushe a girgizar kasar wacce ta afku a Kudancin kasar ta Turkiyyar.

Wannan labari na zuwa ne bayan da adadin wadanda suka mutu a bala'in ya karu zuwa 432 inda kuma dubun dubatar mutane suka rasa gidajensu. Girgizar kasar dai ta afku ne a gundumar Van ranar Lahadi da yamma - kuma karfinta ya kai maki bakwai da digo biyu.

Har yanzu dai masu aikin ceto na ci gaba da yunkurin ceto wadanda lamarin ya ritsa da su.

Masu aikin ceton dai sun waye garin ranar Talata suna yunkurin zakulo wadanda gine-gine suka rufta da su, inda suke amfani da karnuka masu sansano jama'a.

Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce fatan da ake da shi na gano wadanda abin ya ritsa da su a raye, na kara dusashe wa.

Karin bayani