UNESCO zata yi mahawara akan Falasdinu

Hakkin mallakar hoto Getty

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin duniya, Ban Ki-Moon, ya bayyana damuwa a kan bukatar da Falasdinawa suka mika ta neman cikakken wakilci a Hukumar Ilimi, da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO.

Matakin wani bangare ne na gangamin da Falasdinawan ke yi na samun cikakken wakilic a matsayin kasa, a Majalisar Dinkin Duniya ita kanta.

Matakin dai ya biyo bayan cikas din da ake samu ne a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Falasdinawan da Isra'ila.

Amurka, wadda ke bai wa UNESCO gudummuwar kashi ashirin da biyu a cikin dari na kasafin kudinta, ta yi barazanar daina ba da gudumuwar idan aka amince da cikakken wakilcin Falasdinun.