NTC ta shedawa NATO -Ku ci gaba da zama a Libya

Shugaban majalisar rikon kwaryar Libya, Mustapha AbdelJalil ya ce, ya na san dakarun NATO su ci gaba da aikinsu a Libya har zuwa karshen shekara.

Da yake magana bayan wani taro da akai a Qatar, Mr. Jalil ya ce yana san NATO ta tsaya domin hana magoya bayan Kanar Gaddafi ficewa daga kasar.

Ya ce, "mu mutanen Libya gaba daya na son kawancen ya ci gaba da aikinsa har zuwa akalla karshen shekara"

Amma kuma muna neman taimakon abokanmu su taimaka mana wajen kare kan iyakarmu.

A ranar juma'a ne ake sa ran NATO za ta yanke shawarar lokacin da zata dakatar da ayyukanta a Libya.

Kawancen dakarun NATO dai sun yi ta kai hare hare ta sama kan dakarun marigayi Kanar Gaddafi a iya tsawon lokacin da aka kwashe ana rikici a kasar.