'Pakistan na goyon bayan 'yan Taliban'

Hakkin mallakar hoto none
Image caption 'Yan kungiyar Taliban

Wani bincike da BBC ta gudanar ya bayyana cewa kasar Pakistan tana goyan bayan 'yan kungiyar Taliban don yakar dakarun Amurka da ke Afganistan.

Mayakan Taliban da dama sun shaidawa BBC cewa jami'an kasar Pakistan ne suke basu horo na musamman kan yadda za su hada bama-bamai.

Dakarun Amurka da ke kusa da iyakar Pakistan, sun ce sun ga sojojin Pakistan suna taimakawa 'yan Taliban.

Da ma dai Amurka ta shafe shekara da shekaru tana yi wa Pakistan kallo a matsayin wacce ke goyon bayan masu tayar- da- kayar- baya da ke yakar sojojinta da ke aiki a Afghanistan.

Pakistan din ta sha musanta wannan zargi.