Yawan jama'a na barazana ga duniya

Yara a India Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu jarirai a India wacce na daga cikin kasashen da suka fi yawan jama'a a duniya

A ranar talatin da daya ga watan nan na Oktoba ne ake sa ran yawan jama'ar duniya zai kai biliyan bakwai, wato miliyan dubu bakwai.

A duk rana adadin bil'adama kan karu a doron kasa, duk kuwa da matakan kayyade iyali ko takaita haihuwa da ake amfani da su a kasashe daban-daban. Idan kana tababa, leka wuraren hada-hadar jama'a.

Wakilin BBC a jihar Enugu ta Najeriya, AbdusSalam Ibrahim, wanda ya leka wata kasuwa a garin, ya ce babu shakka jama'ar da ke hada-hada a wurin na karuwa a kullum.

Ya kara da cewa da haka ne kuma adadin jama'ar duniya ke cika biliyan bakwai a karshen wannan watan na Oktoba.

Kalubale

To ko akwai isasshen abinci ga kowa da kowa da ke cikin wannan adadi? Mista Denis Agbo, wani magidanci, ga kuma abinda ya shaida wa BBC:

"Wasu mutanen suna da isasshen abinci, wasu suna na da shi dan kadan, wasu kuwa suna matukar fuskantar matsalar samun abin da za su ci.

"Saboda ba su da kudin sayen abincin, kuma basa iya noma abin da za su ci, domin wasu suna zaune ne a maraya inda babu gonaki. A kauyuka kuma matasa suna ta kaurace wa harkar noma".

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Najeriya ta fi kowacce kasa yawan jama'a a nahiyar Afrika

Ruwa

Ruwa, akan ce abokin aiki, wanda ba shi abokin gaba!

To ko shi ma ya yalwaci jama'a, domin sha da sauran bukatun yau da kullum?

A ganin Mrs Lucy Okafor, wata macen aure, a yanzu kam ana fama da karancinsa a galibin wurare:

"Dalili kuwa shi ne a da can ba a da yawan jama'a, ba masana'antu da yawa, ga otal-otal barkatai.

"Amma yanzu duk wadannan abubuwa sun yawaita, musamman a alkaryu kamar Enugu. kusan ko'ina. Gwamnati kuma ba ta iya wadata kowa da isasshen ruwa".

Muhalli

A duk inda ka zagaya birni da kauye, za ka tarar ana aikin gina gidaje. Shin ko hakan na nufin muhalli ya wadaci jama'ar duniya?

Mista Paul Onyekwere, wani magidanci yana ganin ba haka ba ne:

"Saboda sai ka ga iyalin da suka kai mutum goma sha biyu, suna kwana a daki daya, cakude da iyayen da yara manya.

Hatta a kauyuka ma mutane da dama suna rakube ne a gidajen iyayensu, duk kuwa da cewa ya kamata a ce sun sami nasu muhallin daban.

A yanzu dai ba mu san inda aka dosa ba, domin gwamnati ba ta wani abin a zo a gani game da muhalli don talaka".

Sai dai Mista Chukwudi Achife, daraktan yada labarai na gwamnan jihar Enugu, ya ce gwamnatinsu na yin iya bakin kokari ta fuskar bunkasa harkar noma da samar da ruwan sha, tare da bullo da wasu shirye-shirye don samar da gidaje musamman ga kananan ma'aikata.

Haka gwamnatocin sauran jihohi da ma gwamnatin tarayya, duk sukan bayar da irin wannan alwashi.

To, ko ana gani a kas? Wadanda akan yi dominsu ne kadai ka iya bayar da amsa.

Karin bayani