Yawan jama'ar duniya zai kai biliyan bakwai

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto wanda a ciki take bayyana kalubalen da ake fuskanta a sakamakon karuwar yawan jama'ar duniya.

Hakan na zuwa ne gabanin fitar da wani rahoto ranar 31 ga watan nan na Oktoba, lokacin da majalisar dinkin duniya za ta yi hasashen cewa yawan al'umar duniya zai kai bilyan bakwai.

Fiye da shekaru goma ke nan da yawan al'ummar ya haura bilyan shidda, kuma adadin na karuwa da mutane dubu dari biyu a kowace rana.

Rahoton na cewa maimakon a rika koken ko yawanmu ya wuce kima, kamata yayi a maida hankali wajen irin matakan da suka kamata a dauka wajen kyautata yanayin zamantakewa.

A cikin rahotanta na shekara-shekara a kan yawan jama'a a duniya, hukumar ta bayyana hanyoyin da za a inganta rayuwar jama'a, waadanda suka hada da ilimi da samar wa matasa aiki da kula da wadanda suka manyanta, da samar da ruwan sha, da tsara birane da kuma takaita haihuwa.

Majalisar dinkin duniya ta ce bai wa mata 'yanci da buda masu hanyoyin ci gaban tattalin arziki suna da muhimmanci wajen daidaita karuwar yawan jama'ar tare da kawo karshen talauci.