Rikicin euro: Hannayen jari sun tashi

Rikicin Euro: Hannayen jari sun tashi
Image caption Shugabannin Turai sun yi alkawarin ceto yankin na Euro

Darajar hannayen jari ta tashi sosai bayan da shugabannin Turai suka amince da wani shiri da suka ce zai taimaka wajen shawo kan rikicin tattalin arzikin yankin.

Kasashen da ke amfani da kudin euro sun amince su fadada asusun ceto tattalin arzikin yankin sannan bankuna su yafe wani sashi na basukan da suke bin kasar Girka a maimakon sake karfafa jari.

Manyan kamfanonin da darajarsu ta daga sun hada da bankunan Faransa, wadanda sune kan gaba wajen baiwa Girka bashi.

Darajar hannayen jarin Credit Agricole ta tashi da kashi 21 sannan Societe Generale ya tashi da kashi 16.

Barclays ya tashi da kashi 13, sai Deutsche Bank da ya tashi da kashi 15 dukkansu dai cikin dari.

A Girka ma....

BNP Paribas na Faransa shi ma ya karu da kashi 16.6 yayin da Royal Bank Of Scotland na Burtaniya ya tashi da kashi 12.

Darajar takardar kudi ta euro ma ta tashi idan a kan dalar Amurka da kuma fan na Burtaniya.

A birnin Athens na Girka, cibiyar rikicin, hannayen jari sun tashi da kashi 4 da digo 8.

Wasu daga cikin bankunan kasar sun samu tagomashi da fiye da kashi 10 cikin dari.

Kasuwannin hada-hadar kudi sun sha fuskantar koma baya a Turai da Asia a bana kan tsoron cewa ba za a iya shawo kan rikicin ba, kuma mai yiwuwa Girka ta kasa biyan basukan na ta.

Karin bayani