Ambaliyar ruwa ta halaka mutane goma a Ghana

Image caption Taswirar kasar Ghana

Shugaba John Atta Mills na Ghana yayi alkawari daukar matakin hana sake afkuwar ambaliyar ruwa a Accra, babban birnin wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 10.

Yayi alkawarin cewar Gwamnati za ta dubi hanyoyin bayar da kudi domin gina sababbun magudanan ruwa.

Ya ce abu ne da ba za a amince da shi ba a gina gidaje a kan hanyoyin ruwa, bisa sabawa dokokin tsarin birane.

Ambaliyar ta ranar laraba ta lalata gidaje da yanke wutar lantarki da kuma malale hanyoyi.

Masu aiko da rahotanni sun ce ba kasafai ake ganin saukar ruwan sama mai karfi a kasar a irin wannan lokaci ba.

Damina a kasar dai tana fara kankama ne daga watan Yuni zuwa watan Agusta.