Mutane shida sun mutu a Ghana

Image caption Taswirar kasar Ghana

Mutane shida ne suka mutu bayan saukar ruwan sama mai karfin gaske, wanda ya janyo ambaliya a Accra, babban birnin kasar Ghana.

Magidanta sun rasa inda za su saka kawunansu, yayin da koguna suka rika cika suna batsewa, al'amarin da ya yi sanadiyyar rushewar gidaje.

Ruwan saman dai ya shafe akasarin titunan birnin.

Masu aiko da rahotanni sun ce ba kasafai ake ganin saukar ruwan sama mai karfi a kasar a irin wannan lokaci ba.

Damina a kasar dai tana fara kankama ne daga watan Yuni zuwa watan Agusta.