Ministan wasannin Brazil ya yi murabus

Image caption Orlando Silva

Ministan ma'aikatar wasannin kasar Brazil, Orlando Silva, ya sauka daga kan mukaminsa bayan an zarge shi da aikata cin hanci da rashawa.

Ana zargin Mr Silva ne da sauya akalar wasu kudade da aka warewa kungiyoyi masu zaman kansu a ma'aikatar, inda ya rika amfani da su wajen daukar nauyin jam'iyarsa maisuna Communist Party of Brazil.

Ministan dai ya musanta zarge-zargen. Mr Silva shi ne aka dorawa alhakin shirye-shiryen gasar wasan cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a yi a kasar a shekarar 2014.

Mr Silva dai ya sha sukar hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, FIFA, saboda abin da ya kira yawan tsoma bakinta kan batun daukar nauyin gudanar da gasar kwallon kafa da kasar za ta yi a shekarar 2014.