Jama'iyar farar fata ta zabi wata baka a matsayin shugabarta a Afrika ta kudu

A karon farko, babbar jam'iyyar adawa a Afrika ta kudu, ta Democratic Alliance ta zabi bakar fata a matsayin shugabar ta a majalisar dokokin kasar.

An zabi matar ce mai suna Lindiwe Mazibuko, mai shekaru 31 wadda shugabar jam'iyyar ta kasa, Helen Zille, ta goyi bayan bukatarta.

Wakilin BBC a Cape Town ya ce har yanzu jam'iyyun adawa a kasar na kokorin sauya kallon da ake yi masu na jamiyyun turawa, shekaru 17 bayan kawo karshen mulkin wariyar lauyin fata.

Masu sukar zaben nata sun bayyana sauyin a matsayin wani na jeka- na - yi-ka.