Sudan ta goyi bayan 'yan tawayen Libya

Umar al-Bashir Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sudan da Libya sun dade ba sa cikakken shiri

Shugaban Sudan Umar al-Bashir ya ce kasarsa ta baiwa 'yan tawayen Libya wadanda suka kifar da gwamnatin Kanal Mu'ammar Gaddafi taimakon soji.

A wani jawabi da ya yi kai tsaye ta talabijin ga 'yan kasar, Mr Bashir ya ce matakin wani martani ne ga goyon bayan da Gaddafi ya baiwa 'yan tawayen Sudan shekaru uku da suka wuce.

Sudan da Libya sun shafe shekaru da dama suna fama da rashin jituwa.

An bayyana 'yantar da Libya ranar Lahadi, kwanaki biyu bayan an kashe Kanal Gaddafi .

Shugaba Bashir ya ce shekaru uku da suka wuce, 'yan tawaye na kungiyar Justice and Equality Movement (JEM), daga yankin Darfur, sun kai hari birnin Khartoum, inda suka yi amfani da makamai da kudi daga kasar Libya.

Ya ce Alla ya baiwa Sudan damar ramawa, ta hanyar tura nmakamai, da alburusai da kuma kayan jinkai ga 'yan tawayen Libya.

'Ramuwar gayya'

"Allah madaukakin Sarki, ya bamu damar rama abin da aka yi mana," a cewarsa.

"Dakarun da suka shiga birnin Tripoli, sun yi amfani da wasu makamai wadanda dari-bisa-dari na Sudan ne," kamar yadda ya jaddada.

Shugaban JEM Khalil Ibrahim ya taba zama na wani lokaci a Kudancin Libya.

Amma yanzu ya koma Darfur, inda ake ci gaba da yakin da aka shafe shekaru takwas ana gwabzawa.

Kalaman na Mr Bashir sun nuna yadda yake son kulla alaka da sabbin shugabannin na Libya.

Sai dai yawaitar makamai a Libya, da kuma iyakar da kasar ke da ita da yankin Darfur, na barazana ga mahukuntan Sudan.

Karin bayani