Maza da mata daya ne a masarautar Birtaniya

Pira ministan Birtaniya, David Cameron, ya bayyana cewar kungiyar kasashe renon Ingila ta Commonwealth, ta yanke shawarar kawar da nunin banbanci tsakanin maza da mata da kuma addini na shekaru aru -aru a gadon masarautar Birtaniya.

Kasashe 16 na kungiyar Commonwealth baki daya sun amince cewar ya kamata mata a gidan Sarautar su kasance da yanci daya da maza.

Sauyin na nufin yaro na miji ko mace,na farko ga Yarima William da matarsa Kate Middleton ne zai kasance na farko a jerin magadan sarautar.

Baya ga batun masarauyar Ingila, mahalarta taron na Commonwealth kuma za su tattauna kan matsalar tattalin arzikin kasa da kuma sauyin yanayi.