An kashe mutane 37 a zanga zangar Syria

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sunce akalla fararen hula 37 ne aka kashe bayan masu zanga zanga sun fantsama a tituna suna bukatar a sanyawa kasar haramcin zirga-zirgar jiragen sama.

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin Bil Adama ta Syria ta ce an yi zanga zanga a Homs da Qamishly a arewa da kuma Deraa a kudanci.

Haka kuma akwai rahotanni na yin artabu a Hama tsakanin yan adawa da dakarun tsaroGwamnati ta zargi kungiyoyin masu daukar makamai da kai hari a kan Ofishin yansanda a Homs.

Ba dai san ainihin dalilin mace - macen ba, kuma ba abu ne mai saukin tantance rahotanin ba saboda Syria ta saka takaici mai tsauri a kan kafofin watsa labarai.