Shugaba Assad ya gargadi kasashen yamma

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya gargadi kasashen yammacin duniya da kada su yi katsalanadan a Syria, yana mai cewa idan suka kuskura suka yi hakan to za su haddasa wata girgizar kasa wadda za ta kona daukacin yankin Gabas ta Tsakiya.

Masu zanga-zangar kin jinin ginin gwamnati ne dai suka yi kira ga kasashen duniya su haramta tashi da saukar jiragen sama a kasar ta Syria, amma a hirar da wata jaridar Birtaniya mai suna Sunday Telegraph ta yi da shi, Sugaba Assad ya ce yanzu dakarunsa da 'yan ta'adda suka fada.

Masu fafutuka sun ce an kashe fararen hula fiye da ashirin a tashe-tashen hankulan da suka auku ranar Lahadi daura da birnin Homs na tsakiyar kasar.

Akwai yiwuwar dai kasashen yamma su kai hari a Syria, ganin cewa an gama da Libya, kuma hankulan jama'a da dama ne ya karkata zuwa kasar, musamman ma yadda 'yan adawa a kasar ke bukatar haka.

Katsaladan

Hakan dai na iya faruwa ne idan aka la'akari da irin zub da jinin da ake yi a kasar.

A wata hira da ya yi da jaridar Sunday Telegraph, Shugaba Assad ya yi gargadin cewa kasar Syria ba daya take da sauran kasashen Larabawan da ake boren kin jinin gwamnati ba.

Ya ce Syria tana tsakiyar yankin ne, kuma duk wani yunkuri da aka yi na tsoma baki a al'umuran kasar na iya janyo girgizar kasa a yankin, wanda zai zamo babban matsala ga yankin gabaki daya.

Mista Assad ya ce ya gudanar da sauye sauye a kasar wadda suka daidaita al'umura, kuma hakan ya samu goyon bayan jama'a da dama, inda ya ce abun da ya rage kadai shine ya kawar da 'yan ta'ada.

Amma masu fafutukar kare hakkin bil adama sun ce an kashe sama da fararen hula ashirin a ranar asabar a ciki da kuma kusa da garin Homs a arewacin Damascus.

A garin Homs da Idlib da kuma can arewa masu sa ido a harkokin kare hakkin bil'adama a kasar sun ce an kai hare-hare akan jami'an tsaro inda aka kashe akalla 30 daga cikinsu.

Wani kwamadan sojin Syria wanda ya sauya sheka, Kanal Riad al-Asaad ya shaidawa BBC cewa dakarunsa ne wadanda da dama sojoji ne da suka sauya sheka su ke kai hare haren a fadin kasar akan jami'an tsaro.