Masar ta shiga tsakani a rikicin Falasdinu da Isra'ila

Image caption An kashe mayakan sa kai tara a Gaza

Rahotanni sun ce kasar Masar ta shiga tsakani kungiyoyin mayakan sa-kai na Zirin Gaza da Israila sun tsagaita bude wuta.

Yarjejeniyar dai ta zo ne bayan hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza ranar Asabar da kuma wadanda ta kai da sanyin safiyar ranar Lahadi sun hallaka mayakan sa kai tara na kungiyar Islamic Jihad, yayin da wani dan Isra'ila daya ya rasa ransa a garin Ashkelon.

Tun da farko dai wani mai magan da yawun kungiyar ta Islamic Jihad ya ce za su dau fansa:

Ya ce; "Mu a kungiyar Islamic Jihad za mu dorawa Isra'ila alhaki dungurungum na duk abin da zai faru a 'yan kwanaki masu zuwa."

Wannan tashin hankali dai shine mafi muni da aka yi tun bayan da aka yi musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas a farko wannan wata. Hamas dai ce ke mulkin yankin Gaza a kasar Falasdinu.

Idan har bangarorin biyu dai su ka tsaigata wuta, hakan zai kawo karshen zub da jinin da ake yi tsakanin bangarorin biyu tun bayan wanda aka yi tsakanin masu fafutuka a Gaza da kuma Isra'ila a karshen watan Agusta.

Wani mai magana da yawon hukumar bada agaji a Gaza ya ce harin farko da Israila ta kai a ranar asabar ya yi sanadiyar mutuwar membobi kungiyar Al-Quds su biyar a yayinda guda uku su ka jikkata.

Mahukanta a Falasdinu dai sun ce harin cikin dare da Isra'ilan ta kai ya kara kashe masu fafutuka hudu a yayinda mutane biyu kuma su ka jikkata. Isra'ila dai ta ce sojojin ta sun kai hare hare ne akan 'yan ta'ada a Gaza domin hana su ci gaba da harba rokoki cikin Isra'ila.