An fara shari'ar jagoran Kill Team

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Amurka a Afghanistan

An fara shari'ar mutumin da ake zargi da jogorantar wasu sojojin Amurka, wadanda su ka kashe fararen hula da dama a kasar Afghanistan, suka kuma ajiye wasu sassan jikinsu, bayan sun kashe su.

Ana dai shari'ar Staff Sergent Calvin Gibbs ne a wata kotun soji, inda ya ki ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Idan har aka samu Sergeant Gibbs da laifi za a daure shi har tsawon rayuwarsa.

Wasu sojoji uku dai sun amsa laifi kuma sun ce za su gabatar da shaidu a kan Sergeant Gibbs.

Masu shigar da kara na Soji sun ce a lokacin da sojojin Amurkan ke kudancin Afghanistan a bara.

Sergeant Gibbs ya jagoranci sojojin ne wadanda su kai ta kashe fararen hula ba gaira babu dalili da sunan suna wasanni.

Ana dai zargin sojojin ne da cire wasu sassan jikin wadanda suka kashe a matsayin ganima, sannan kuma suka shirya gwawakinsu tamkar sun kashe su ne yayin da suke kare kansu.

Sergeant Gibbs dai bai amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

Ana alakanta wannan batu dai da irin ta'asar da sojojin Amurka suka aikata ta cin zarafin jama'a a gidan kason Abu Ghraib da ke kasar Iraqi.

Jami'an Petagon kuma sun bayyana al'amarin a matsayin babban abun kunya ga sojojin Amurka a duniya gabaki daya.