An dage shara'ar Mubarak

Hakkin mallakar hoto AFP

An dage shariar da ake yiwa tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak, har zuwa karshen watan Disamba.

An bada sanawar jinkirta shariar ce yayinda ake cigaba da tattaunawea kan ko a maye gurbin alkalan dake yi ma shi sharia, sakamakon koke-koken da aka samu daga lawyoyin dake kare iyalan wadanda aka kashe a lokacin jerin zanga-zangar da jamaa suka yi na nuna adawa da gwamnati, a farkon wannan shekarar.

Ana dai zargin Mr Mubarak ne da wasu mukarrabansa da hannu a kisan wasu daga cikin masu zanga-zangar. Ya'yansa maza biyu kuma, an tuhume su da laifin cin hanci da rashawa.