Ma'aikatan Qantas na yajin aiki

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Australia Qantas, ya dakatar da tashin dukan jiragensa saboda wani takun saka da ya ke yi da kungiyoyin kwadago.

Ma'aikatan kamfanin na Qantas dai sun yi yajin aiki dangane da batun albashi da yanayin aiki da kuma wani shiri da kamfani na Qantas ke yi na mayar da wasu guraben aiki zuwa kasashen waje.

Piraministar Australia, Julia Gillard, ta yi gargadin cewa wannan takaddama za ta iya yin illa ga tattalin arzikin kasar.

Yajin aikin da ma'aikatan kamfanin na Qantas ke yi dai, yana yin barazana ga jigilar shugabannin kasashen Commonwealth, inda aka shirya wasu daga cikinsu za su tashi ne cikin jiragen na Qantas domin komawa gida, bayan sun kammala taronsu a gobe Lahadi.