Saif al Islam ya musanta zargin da ake yi masa

Saif al-Islam Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan marigayi kanal Gaddafi

Babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya ce dan Kanar Gaddafi, Saif al-Islam ya musanta zargin da ake yi cewa ya aikata laifin cin zarafin bil Adama a lokacin yakin basasar kasar Libya.

Luis Moreno Ocampo ya ce Saif al-Islam ya hakikice yayin wata tuntubar juna da masu shiga tsakanin na kotun cewa ba shi da wani laifi.

Sai dai Mista Ocampo ya ce yana fargabar Saif al-Islam zai sauya shawara ya tsere zuwa wata kasa:

Ya ce; "Mun samu labarin cewa wata kungiyar sojojin haya na kokarin tainmaka masa ya tsere zuwa wata kasar ta daban muna kuma kokarin hana faruwar hakan."

A wata sanarwa da ya fitar, babban mai gabatar da kara na kotun Luis Moreno Ocampo ya ce idan saiful Islam ya mika kansa, kotun zata saurarreshi kuma za'a bashi damar kare kansa.

Ranar alhamis, an ruwaito wani jami'in Nijar yana cewa Saiful Islam yana kusa da iyakar kasar Nijar da Libya, inda wasu azbinawa ke masa goma ta arziki.