An kashe mutane 75 a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP

Akalla mutane 75 sun hallaka wani hari da mayakan wata babbar kungiyar 'yan tawaye a Sudan ta Kudu, ta SSLA suka kai hari a kan wani gari dake jihar Unity mai arzikin man fetur.

Kakakin dakarun sojin Sudan ta kudu ya fadawa BBC cewa sojojin gwamnati 9, da farar hula 15 da kuma dakarun 'yan tawaye 50 ne suka mutu a karawar da akayi.

Amma kuma 'yan tawayen sunce sun hallaka sojojin gwamnati dari-bakwai. Koda yake da wuya a iya tabbatarda wannan adadi.

Babu wata kafa mai zaman kanta data tabbarda ikirarin da bangarorin 2 keyi.

Kungiyar SSLA din dai ta farma garin MAYOM ne da safe, kuma tace tuni da karbe iko dashi.

Sai kuma kakkain sojin kasar, ka kantoman garin, dakuma wani mazaunin garin duk sun shaidawa BBC cewa an fatattaki 'yan tawayen.

A ranar juma'ar da tagabata, 'yan tawayen sun baiwa ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya mako guda da su fice daga jihar Unity.

Ko da yake kungiyoyin tawaye sun cimma yarjejeniya da gwamnati tun da Sudan ta kudu ta zama kasa mai 'yanci, amma kuma haryanzu akwai wasu 'yan tawayen da suka cije