Qantas ya fara jigilar fasinjoji

Image caption Ma'aikatan kamfanin jirgin saman sun shiga yajin aiki ne a ranar asabar

Kamfanin jirgin saman Qantas da ke Asutrailia ya fara jigilar fasinjoji bayan da wata kotu dake sauraren karraki da suka shafi kwadago a Austrialia ta yanke hukuncin kawo karshen yajin aikin da kungiyoyin kwandagon kamfanin jirgin saman su ka shiga.

Kungiyoyin kwadagon dai sun ce za su yi aiki tare da kamfanin domin ganin cewa ya fara aiki kamar yadda ya saba a baya.

Yajin aikin da ma'aikanta kamfanin jirgin saman Qantas su ka shiga ya gurgunta harkar zirgar-zirgar jiragen sama a kasar.

Shugaban kamfanin jirgin saman, Alan Joyce, ya ce kamfanin yana duk mai yiwuwa domin ganin al'amura sun daidaita.

Ya ce ; "Za mu kara ma'ikata a filin jiragen sama domin taimakawa kwastamomin mu.

"Muna kara duba karfin ma'ikatan mu domin gudanar da ayyukan da za su share ayyukan da su ka taru a baya, saboda yajin aikin.

"Zamu kara yawan jiragen da jigilar kasa da kasa da jirage hudu, Kuma nan da kwana daya muna fatan abubuwa za su dawo kamar yadda su ke a baya." In ji Alan Joyce

Mr Joyce dai ya baiwa fasinjoji sama da dubu saba'in hakuri da yajin aikin da aka fara a ranar asabar ya shafa.

Ya ce; "Ina kara ba kwastamomin mu hakuri, Muna matukar nadamar da tashin hankali da rashin jindadin da wannan al'amari ya janyo."

"Zamu yi duk abun da ya kamata domin ganin abubuwa sun daidaita cikin lokaci."

Ma'aikatan kamfanin na Qantas dai sun yi yajin aiki ne dangane da batun albashi da yanayin aiki da kuma wani shiri da kamfani na Qantas ke yi na mayar da wasu guraben aiki zuwa kasashen waje