Rikicin bashin Turai na iya shafar bankuna

Kasuwar hannayen bankunan Turai

Darajar hannayen bankuna sun fadi a kasuwanni da dama, bisa tsoron tasirin da rikicin bashin kasashe masu amfani da kudin euro ka iya yi. A London, hannayen jarin bankunan Royal Bank of Scotland da Lloyds, suka fadi da kashi bakwai.

A Amurka kuwa, hannayen jarin Bank of America ne suka fadi da kusan kashi biyar.

Sannan babban kamfanin zuba jari MF Global, ya nemi a bashi kariya bayan da ya bayar da bashin kudade masu yawa ga kasashen Euro.

Wakilin BBC yace babbar matsalar MF Global, ita ce jarin dala biliyan shida da ya zuba a basukan wasu kasashen Turai dake tangal-tangal - duk da cewa babu kasar Girka a ciki.